KYAUTAR ALLAH A Asibitin Nasarawa 12:00pm 1. Al-raziqu godiya zani zana, Don wagga kyauta da kayyo gurina. 2. Nai godiya da isowar Amina, Kyautar mutum ba kamarta gurina. 3. Nau’in wadata idan anka tona, Gida biyu yakkasu a sanina. 4. Allah ya ce Almali wal banuna, ‘Ya’ya da dukiyya cikin Qur’ana. 5. Zinatul Hayatul dunya bayana, Su ne adon rayuwar duniyar na. 6. Baiwarka ta shallake hankalina, Rahamarka na mamaye ko a ina. 7. Kyautar da kai min a yau Khaliqina, Tahamida nake maka Khaliqina. 8. Raina ya yi tas! A wannan fa rana, Da tai yi daidai da Juma’ar bana. 9. Sunan xiya Juma suna na rana, Suna na yanka ko ace Amina. 10. Kullum idan nai waya ko da rana, Sai tambaya yaushe zan kon Amina. 11. Yau gashi Allahu ya yanke rana, Ranar zuwa duniya ta Amina. 12. Sha takkawas ga watan shida bayana, Shekara dubu biyu goma kana. 13. Sulusin dare da xigonnin mintuna, 1 www.PDFCool.com Loto na sauka ta Juma Amina. 14. Allah ya albarka ce ki Amina, Yasa ki zam a cikin salihina. 15. Jinqansa Allah Maqagi na raina, Ya sallaxa gun ki ki yi alfana. 16. Jinqan Iyaye cikin so da qauna, Ki zam a xiyar da bata khiyana. 17. Allah ya albarkaci ahalina, Ya haxxa kanku cikin so da qauna. 18. Ko da ina raye ko babu raina, Ya kauda tasku a kanku xiyana. 19. Ya sa ku rayu qarqashi na sunna, Sunnar Ma’aiki Nabi xan Amina. 20. Tamat da sunanka Allah Gwanina, Na kattama baituka don Amina. 21. Yau gashi mai juya safe da rana, A kwana a tashi an kai ga Rana. 22. Mai za ni ce gun Maqagin Amina, Alhamdulillahi ya Khaliqina. 23. Ka bani ‘ya’ya Mazaje gurina, Ka bani mata ciki ga Amina. 24. Ka hore ikon tufa ta su guna, Ka bani gurbin muhalli na kwana. 25. Ka yassare min abincinsu guna, Dare da safe zuwa hudo Rana. 26. Babban jidalin da yassaura guna, In basu tarbiya dare da Rana. 2 www.PDFCool.com 27. Allah riqa min ka shiryan xiyana, Wayo tsumi illimi babu guna. 28. Kai ka issa kai kaxai Khaliqina, Shirya tana gunka mai tsaida Rana. 29. Wanda ka shirya shi ba mai hiyana, Da zai vatarshe shi jinni in sana. 30. Allah haxan kawuka na xiyana, Tun kan zuwan mai rabe so da qauna. 31. Suna na Autar xiyata Amina, Mai binta Aishattu Kaka gurina. 32. Ga Hussuna ga Muhsin Hasna, Zahra’u Bilkisu Momi gurina. 33. Qarshe na sanyo rabo a gurina, Fauzul Azimu rabo ne gurina. 34. Allah haxe kawuna na xiyana, Tun rayuwa kan zuwan qare kwana. 35. In na wuce kui du’a’i a guna, Kullum ku zam yin du’a’i gurina. 36. Allahu nai godiya Murabbina, Har-haxa kayinsu ‘ya’ya a guna. 3 www.PDFCool.com
© Copyright 2025 ExpyDoc