AMINIYA Juma’a,12 ga Disamba, 2014 [ Adabi Adabi [ 33 Tare da Bashir Yahuza Malumfashi [email protected] (08098157899) Waqe: Allah Ka ba mu zaman lafiya Babu shakka al’amura sun kai intaha, zaman lafiya ya qaura daga Najeriya, musamman ma a yankunan Arewa. Kullum rana ta lillahi sai an samu labarin tashin hankali, sai an samu labarin mutuwar al’umma da asarar dukiya. Kamar yadda aka sani, babu wani abu da zai yi tasiri a rayuwa, idan babu zaman lafiya. Al’umma suna cikin tsoro da fargaba, wasu sun zama ’yan gudun hijira a cikin qasarsu; wasu kuwa sun ma gudu sun bar qasar tasu ta haihuwa. Babu abin da mutane ke buqata sai zaman lafiya, wanda shi ne abu mafi alheri a rayuwa. domin ganin an samu zaman lafiya, Dokta Tilde ya xauki alqalaminsa ya kwarara baituka casa’in da tara, wato xari xaya ba xaya, kamar haka: Daga Dokta Aliyu U. Tilde Su je makaranta su qona ta kurmus Da yara cikinta ga baki xaya. Ta’ala qadiri Ka ban lafiya In rera waqen zaman lafiya. Su ce musu arna da Kalmar Shahada A baki, su fille su ba yafiya. Ka ba ni hazaqa har da fasaha Gurin rera waqar zaman lafiya. Boko Haramunga sun mana illa Sun ci amanar zaman lafiya. Tsira aminci su tabbata gun Muhammadu manzon zaman lafiya. Sun watse birni kaza har da qauye Kowa ta kai nai yake tafiya. Ba shi kaxai ba har da sahabbai Da aluh da matansa baki xaya. Iyali su watse da dangi hakan nan Kowa a firgice sai tafiya. Ya bar wasiyya ga umma tasa Su zanka shiri don zaman lafiya. Da muggan xiya cikin namu soja Ba su da niyyar zaman lafiya. Ya zo da saqo na jalla gare mu Islam nufinsa zaman lafiya. A qauye birane misalinsu Baga Sun yi ta gilla ga baki xaya. Jigo biyar ne inji Muhamman Biyo ni ka ji su ga baki xaya. Sun kashe yara, sun qona mata Sun kauda daxin zaman lafiya. Farkonsu Kalmar Shahada ka gane Biyayya ga Allah zaman lafiya. Ta’ala mashiryi ga ni gare Ka Ina zanka roqon zaman lafiya. Yarda da saqon Muhammadu shi ma Ya na kai ga turbar zaman lafiya. Gare ni da ’ya’ya da mata dukkanmu Da dangi abokai ga baki xaya. Na biyyunsu Sallah na khamsu biyar ne Da ba su yuwa sai akwai lafiya. Musulmi, Kirista Ta’ala Karimu Haxa mu zumuncin zaman lafiya. Ga Ramalana mu zan azuminsa Kaza ba da Zakka zaman lafiya. Daxe mu fahimta ta juna mu gane Cikin arziki ba kamar lafiya. Cikonnasu Hajji ka je in da hali Guzuri da hanyarka mai lafiya. Fitinnu na baya kaza na zamanu Ka kare mu Jalla mu zam lafiya. Sahabi ya ce ya Rasulu gaya mun Zan sam sawaba zaman lafiya? Mu rungumi ilmu na dini da dunya Ci gaban rizqu don zaman lafiya. In na riqe su biyar babu qari? Manzo ya ce har ka zam lafiya. Daxe mu da tsoronKa ya Jalla Sarki Domin Muhamman mijin Mariya. A gobe qiyama a saka a Jannah Nan ne tiqewar zaman lafiya. Ba mu kaxai ba har da Boko Haramun Yaranmu shirye su baki xaya. Ta yaya Musulmi a yau sunka bauxe Wa horo na manzon zaman lafiya? Qanne da yayye cikinsu gaba xai Maido su hanyar zaman lafiya. Su kafirta bayi da Kalmar Shahada Suna rushe saqon zaman lafiya. Ka yafe su laifinsu komai yawansa Bayinka ne Rabbu mai lafiya. Wasunsu gama har makamai gare su Gilla suke ba zaman lafiya. Idan Ka tsane su Allah Gafuru Waye gare su ko a nan duniya? A Yerwa da Bama da Baga da Gwoza Banki, Chibok ba zaman lafiya. Ka nunan da raina ina sintiri Da nono a Yerwa zaman lafiya. Sukan harbe mata da yara da tsofi Samari su sace su baki xaya. In je ni Bama in miqa caffa Gidan Mbusube Baba mai gaskiya. Sukan sace mata da ba su da aure Su auresu karhan suna fariya. Rabbi ka kai ni Gwoza in gan su Mutane na kirkin zaman lafiya. Askira, Uba, Michika in je Qasashe na Margi mutan lafiya. ’Yan kasuwan Bauchi caffa gare ku Ku zauna da himmar zaman lafiya. In shiga Maiha da Mubi in gan su In ba su Waqar Zaman Lafiya. Ku sai mun da nono idan na taho Ku zan yin raha don zaman lafiya. In zo ni Gombi in shiga Hong Har ma da Song don zaman lafiya. In na ga dama in je buga qwallo Wasanmu golf ba ya shi ka jiya? Ku bar ni in zarce wajen Yola dangi Filani na Lamixo mai gaskiya. Safiya ta bani abinci dafaffe Da ’ya’yan itace tana dariya. In kwan salati in je ga Inna Da “Intel” da dukkan maso lafiya. In kwana a gunta cikin so da qauna Ta’ala ka bar mu ga baki xaya. Nuhu Ribaxu aboki amini Ina miqa caffa ga mai gaskiya. Da sassafe in tashi in nufi Tilde Ba ni da haufi cikin tafiya. Da safe in je ni school in gane su Teachers na ilmu cikin lafiya. In isa Toro ga Katuka Sarki Na samai da dangi cikin lafiya. Ga yara da manya musamman ga mata Ci gaba za mui ga baki xaya. Ina ’yan uwana na Tilde ku zo Kuna nan da shauqi kuna tambaya. In shiga mota in kama hanya Zuwa Ganye gun su mutan lafiya. Wata ukku daidai babu Aliyu Cuso na Nana maso lafiya. In je ni in gana da danginmu Chamba Da sarkinsu Gamwari mai gaskiya. Yaro na Fatima har ma da Umma Ga Luba can sun zaman lafiya. In zo ni Numan, na sheqe ayata Baqi na Benue zaman lafiya. Na je can gidanmu in gaida Iro Barhama Ghandinmu mai gaskiya. Timawus Mathias in ganai har ya kaini Gurin nasa gwarzon zaman lafiya. In je kufayi in yi salati Ziyara ga manya gidan gaskiya. Sarkin ‘Bata in yi chaffa gare shi In faxi gu nasa mai gaskiya. In zo ni Zango in tadda ’ya’ya Da mata da dangi suna lafiya. Lamurde zan sayi kifi gasasshe Na cinye a mota zaman lafiya. In yi sujuda in gode Allah Ta’ala ka zaunar da mu lafiya. Ga Tula sun zo da tarba gare ni Suna so in rera Zaman Lafiya. Najeriyarmu gaba xai Afirika Ka ba mu rabo da zaman lafiya. Kaltungo, Villiri har ma da Kumo Ku tashi ku miqe zaman lafiya. Arewarmu Allah ka qare ta ilmu Sana’a amana da son gaskiya. Ku wo dandazon sallama don in gan ku Ku ba ni aron kunnuwan lafiya. Yaranmu Allah Ka shirye su Hadi A hanya tsayayya su so gaskiya. Ku kore su Shaixan ku zan yin zumunci Ku zauna ku miqe cikin lafiya. Manyanmu kau rabbi qare su tausai Na yara, talakka da son mabiya. Zan shiga Kumo domin in gan shi Muhammadu Kumo kana lafiya? Ka kore mugunta cikin zuciyarsu Mayeta da hubbi ga baki xaya. In ba su loto da baya tsawaita Domin in zarce garin gaskiya. Tammat fa waqe a nan zan aje ta Ta cika baiti xari ba xaya. Gombe ta Buba in sadu da dangi Hausa da Fulve gaba ki daya. Mai tambaya za ya ce wa ya yi ta Zan ba ka amsa cikin gaskiya. In shiga Makay in yi sayayya In miqa katina don in biya. Cene Aliyu na Tilde ya yi ta Xan Usmanu mazajen jiya. San Husein da Samaha sai na shige su In qara sayayya, zaman lafiya. A qarshe kirana ga Allah fiyayye Ta’ala Ka tsarshe ni aikin riya. Idan sun ka ce Ya Aliyu ka kwana In ce musu a’a cikin dariya. Ka karvi ibadunmu Rabbi Shakuru Ka kare mu Sarkin zaman lafiya. Zan kwana Bauchi da ikonSa Allah Ta Yakubu garin zaman lafiya. Iyaye jiqan su Ka sa su a Janna Da Alkausara gun zaman lafiya. In isa gu nasa Sarkin garinmu In faxi domin zaman lafiya. Ka qara salati bisa Annabinmu Muhammadu manzon zaman lafiya. In fita fadar ina taqama Na zo gida kana ga lafiya. In je gari in ga Tahir aboki Muhamman Madaminmu mai gaskiya. In nemi Habuna, Sadiqi na Mamman Muhimmi gare ni wajen tafiya. Ahmad Nadani ina zan gane ka Ka ba ni shauqi cikin zuciya. n Dokta Aliyu Tilde, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum
© Copyright 2024 ExpyDoc