DIMOKARAXIYYA DA ADDINI 1. Ya sattaru khaliqi Mabuwayi, Yau fa Aminu ya yi nufin waqa zai yi, Ka taimake ni kar ka cusa mini shayi, In ta ganin kamar ba za ni iya ba. 2. Rabbi salati adadin sumar kai na, Daxa ga wanda za ya cetar min rai na, Ranar da za na rasa gurbin saka kai na, Ran da ba hali bare ayyi manuba. 3. Nai nurin gare mu faxakarwa zan yi, Amma akan dimokaraxiyya zan yi, Don ga shi an saka mu muna ta bulayi, ‘Yan ruxu suna ta cusa mana gaba. 4. Waxansu sun ka ce da mu makirci ne, Wasu kuwa sun ka ce mai yinta mushiriki ne, Wasu kuwa sun ka ce mu yi ta halali ne, In har an ka yi ta za a cire gaba. 5. Wasu sun afka an zubda mutuncin su, Wasu na kyankyamin a kassara ‘yancin su, Don in an ci ba a ko sake kula su, Abin da ya yi saura sai mugun duba. 6. Wannan fa shine ya sa ni xaukar kalami na, In bayyano fa xan kaxan daga hange na, Ko nai kattari su gane dangi na, Abin da za mu yi mu kauce wa akuba. 1 www.PDFCool.com 7. Bari-bari sakato banbanci na aqida, Banbancin gari da yare fa mu kauda, Mu tsaida hankulan mu kalma ta shahada, Allah za ya bamu rinjaye babba. 8. Ina mai tsegumin shigar ta fasadi ne, Masu kira a yi ta Ahlin shirka ne, Don hangen ta masu mugun tsari ne, Yahudu nasara gunmu abokan gaba. 9. Yau mun tsinci kawukanmu a qangi ne, Mun sakaci kwa ko in ce shashanci ne, Dukkan ci gaba a yau Technology ne, Babu abinda ba su yi mana zarra ba. 10. Yau in ka qi ka share gurbin bauta, Ai da rabon ka share gurbi na qazanta, Mutuqar anka ce da ni kai Makaranta, Boko sai in ce zani bata sake ba. 11. Xauki Chemistry da physics kai duba, Ka haxa da Geography dudduba, Za ka ji inda sunka fadar Rabba, Amma Likitan mu su ne yadduba. 12. In fa ana bugun gaba faxa tanka ne, Har da boma-bomai da su aka kaga ne, In har burikanmu dukka jahadi ne, Sai mun tanade su don abokan gaba. 13.In kwa ka so ka san guda ka shiga varna, Abin da ka yi nufi a zuci ka adana, Misali in nufinka toshe kafar varna, Allah ya baka rinjaye babba. 2 www.PDFCool.com 14.Wagga siyasa da kun ka kushe ta, Da ilimin zamanin ga anka tsara ta, Ku da xiyan ku boko duka kun yi ta, Amma yau ku ce mai yi bai kyauta. 15.Kau da batun fa wanga shi ne ra’ayi na, Mu tsaida mafi gudun fushin Ubangiji na, Babu batun fa wagga shine ra’ayi na, Tsarin Allah da Manzo nai babba. 16.Mu haxa kawunan mu kada mu banbanta, Hanyar da ta kauce mu bi ta mu gyara ta, Ku mu yi hazzamu qasar mu mui kishin ta, Kar mu sake a mai da mu ba wayis ba. 17.Ka sani Radio in baka misalinta, In ka ga dama ka so kafirta ta, Za ka jivinci sanya batsa a cikinta, Yarda ka so ka yi ba za ta yi gaddama ba. 18.Haka Television xanuwa ka fahimta, In ka so ganin tsiraici a cikin ta, Kai fa da kan ka za ka tashi ka sarrafa ta, Za fa ka faxxaka a ciki ba aibu ba. 19.Amma in ka so su koma khairi ne, Qur’ani cikin su za ka yi hadda ne, Tafsirai iri daban-daban na mutane, Za fa ka faxxaka a ciki ba aibu ba. 20.Hikima taguwa ku kyautata qauli na, Duk inda mumini ya ganta ya tsuguna, Ya sunguma ya amfana a nufi na, Allah ne ya ba shi ba wani qato ba. 3 www.PDFCool.com 21.Ga wata kissa abar alfaharin mu, Da na samo cikin bukhari sahihinmu, Annabi ne ya tashi wanni sahibin mu, Yassaro fa kan kuffaru mazan gaba. 22.Sahabin ya ce ina ga Rasulillah, Yin haka za ya baiwa uzirin nan matsala, Amma in na aibataka Rasulillah, Za su yi sakkaci in saro maqi Rabba. 23.Ka ga a nan abinda zan so ka fahimta, Varna ce fa aibato baban Binta, Haka nan ma barin fa wanda ya kafirta, Amma an yi don a kau da maqi Rabba. 24.Musulunci fa ya fi dangin iya Baba, Ka da mu sake mu yi masa tsarin ‘yan uba, Ba ai batu na bora mowa ciki nai ba, Bare Agola da ba xanganta ne ba. 25.Mu haxe kanmu tamkar tsinken shara, Ku mu bar hassada ga juna da harara, Al’adunmu da addininmu mu gyara, Ba bagidajen da zai manna manuba. 26.Maqwabci na kussa ko kuwwa na nesa, In yai kalmar shahada bakinsa, Ya zama naka ko ina babu kamarsa, Mai sallah da kafiri ba xaya ne ba. 27.Babu haxi ga wanda ke kallon qibla, Da nufin bauta irin ta Rasulillah, Mushen rago da alhanzir ka kula, Banbancin anan ba ma za a haxa ba. 4 www.PDFCool.com 28.Akwai larurar da kan sa a ci rago, In ya yi mushe a yanka shi da bargo, Alhanzir kwa ai da shi gara qarago, Don shi in ka ci ba bacci haramun ba. 29.Mui xamarar musuluntar da siyasarmu, Kar mu bari a wagga tafiya a aje mu, Mui dandazo da qwanmu da kwarkwatarmu, Mata da mazanmu duk ban ware ba. 30.Nasiha ta ga shugaban da aka zava, Ya dubi Allah fa kar yai yo zamba, Mulkin jama’a ba za fa ya xore ba, Alkhairi ka aikata ko kuwa zamba. 31.Kadda ka xauki shugabanci cin riba, Mulkin jama’a fa ba gado ne ba, Ba dabba ake wa jagoranci ba, Ku sani xan Adam fa ba gunki ne ba. 32.Kuna tafe jiniya ana bubbusawa, Baya da qwuivin ka ga mai qarewa, Ka riqi duniya fa ba ta qarewa, Ba fa anan gizo yake yin sakar ba. 33.Duk wani wanda ba ka so sai ya koka, Don matsayin da anka taru aka sa ka, Za fa ka murqushe shi domin fa isarka, Don bai zavi jam’iyyar da ka ke ba. 34.Da fari ana ta so a ji daga bakin ka, Da ka ci kwa sai a rinqa tsoro da ganin ka, Kowa na gudu na mugun kaidin ka, Mulkin duniya fa ba na qiyama ba. 5 www.PDFCool.com 35.Ba ka kula da masu ma shawartarka, Wane guri su ke ta nema su zura ka, Abokai da ‘yan uwan ka na tashin ka, Kai watsi gare su ba ka ko duba. 36.Ka sani jinjirin da ayyau aka haifa, Har da mahaukatan da yara ke jifa, In faxakar da kai fa babu rufa-rufa, Haqqin su a gunka ba zai zama wai ba. 37.Ka haxa kai da malamai ‘ya’yan duba, In ka ci sai ka kai su watsa sudduba, Wanene yake harin sa maka gubba, Yarda ka ce su yi ba za su yi musu ba. 38.Ko ku biya musu su je can su yi arfa, Su je baitil harami roqo gun gaffa, Nuni na da ku ku san Allah nan fa, Ya fa yi tanadi ga zalinci babba. 39.Ayuhannasi ku muttaimaki kayin mu, Mu gyara hali da dukka xabi’unmu, Yin haka za ya taimaka wa gwamnatinmu, Tai mana maganin abinda ba ta gaza ba. 40.Ku sani ‘yan uwa Aminu na cikinku, Xan Ladan Abubakar ke nushe ku, Na Tudun Murtala gari ne a qasarku, Ala inkiya faxi ba aibu ba. 6 www.PDFCool.com
© Copyright 2025 ExpyDoc